Sanders ya jaddada mubaya`a ga Clinton

Misis Clinton da Minsta Sanders Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Sanders ya yi mubaya'a ga Clinton.

Abokin hamayyar Misis Hillary Clinton a zaben fitar-da-gwanin jam'iyyar Democrats, Sanata Bernie Sanders, ya jaddada mubaya'arsa gare ta a wurin babban taron jam'iyyar.

An yi ta sowa da tafi a lokacin da Mista Sander ke cewa za su ci gaba da gwagwarmayar sauya Amurka, kuma Clinton ce ya kamata ta zama shugabar kasa saboda ta fahimci matsalolin Amurka, da kuma gudunmawar da za ta bayar domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Sanata Bernie Sanders ya kara da cewa za su tabbatar abokin hawayyarsu na jam'iyyar Republican Donald Trump ya sha kaye a zaben da ke tafe.

A cewar Mista Sanders "Trump abin tsoro ne ga makomar kasarmu, don haka dole mu tabbatar bai yi nasara ba, kuma zan ba da duk gudummawar da ta dace wajen yi masa kaye".

Ita ma maidakin shugaban Amurka, Michele Obama, ta yi jawabi mai karfafa zuciya ga mahalarta taron inda ta bukaci 'yan jam'iyyar su hada kai wajen goya wa Hillary Clinton baya.

Ta yaba da halayen 'yar takarar, musamman kwazonta, lokacin da ta rike mukamin Sakatariyar harkokin wajen Amurka, tana mai cewa komai tsananin matsin-lamba Mrs Clinton ba ta kasawa.

Harwayau Michele Obama ta yi habaici ko ga babban abokin hamayyar jam'iyyarsu, Donald Trump, tana cewa Mrs Clinton ta san irin batutuwan da ke gabansu, don haka sun wuce tsayawa cacar-baki da mai kalaman da ba su wuce adadin haruffa 140 da shafin Twitter ke iya dauka, zagin-kasuwar da da ji ka san da Trump ake yi kasancewarsa ma'abocin Twitter.

A wajen wannan taron ne za a tabbatar da Misis Clinton a matsayin 'yar takarar shugaban kasa a tutar jam'iyyar Democrats.