Saudiyya ta daƙile shigar 'yan bindiga

An shafe watanni ana ba-ta-kashi tsakanin Saudiyya da 'yan tawayen Hiuthi na Yemen

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An shafe watanni ana ba-ta-kashi tsakanin Saudiyya da 'yan tawayen Hiuthi na Yemen

Saudiyya ta ce an kashe masu tsaron kan iyakarta biyar a wata ba-ta-kashi da suka yi da wasu 'yan bindiga da suka yi kokarin shiga kasar daga Yemen.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta ce an shafe tsawon sa'o'i takwas ana fadan, bayan da masu tsaron iyakar suka gane cewa mutanen da ke kokarin shiga kasar masu neman tashin hankali ne.

'Yan bindigar sun yi kokarin tsallaka iyakar kasar ne don shiga yankin Najran da ke Kudanci.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan dai ba ta ambaci sunan kungiyar 'yan bindigar ba.

Amma tun watanni 15 da suka gabata ake samun musayar wuta a kan iyaka tsakanin 'yan tawayen Houthi na Yemen da masu tsaron iyakar Saudiyya.