An kaddamar da jirgin kasa mafi gudu a Nigeria

Image caption Shugaba Buhari ne ya kaddamar da sabon jirgin

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da sabon jirgin kasa na fasinja wanda zai dinga zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a wani kasaitaccen biki a ranar Talata.

A yayin bikin kaddamarwar, shugaban ya yi tafiyar minti 18 a jirgin daga tashar Idu zuwa ta Kubwa tare da dumbin jama'a.

Daga nan sai jirgin ya wuce birnin Kaduna a tafiyar kilomita 120 zuwa 150 a duk sa'a daya.

Za a dinga cajin fasinjojin jirgin naira 500 daga Abuja zuwa Kaduna.

Jirgin shi ne irinsa na farko mafi gudu da aka kaddamar a Najeriya, kuma yana yin tafiyar sa'o'i biyu ne tsakanin Abuja da Kaduna.

An bayar da aikin kwangilar jirgin ne tun zamanin mulkin shugaban Cif Olusegun Obasanjo, amma sai a lokacin shugaba Jonathan aka kadaamar da aikin, duk da cewa bai fara aiki a lokacin ba sai a yanzu.

Wannan dalili ne yasa jam'iyyar adawa ta PDP wadda ita ce ta tsohon shugaba Jonathan din take ta wallafawa a shafinta na Twitter cewa a karkashin mulkinta ne aka yi wannan ''hobbasa''.

Ta kuma ce shugaba Buhari ya samu damar kaddamarwar ne kawai amma ba ''kokarinsa'' ba ne.

Labarai masu alaka