Hillary Clinton ta kafa tarihi

Hakkin mallakar hoto AFP

Jam'iyyar Democrats ta zabi Misis Hillary Clinton a matsayin 'yar takarar zaben shugaban Amurka da ke tafe a watan Nuwamba.

Hillary ce dai mace ta farko da ta fara taka wannan matsayi a tsakanin manyan jam'iyyun siyasar kasar.

A wani sakon hoton bidiyo da ta aike wa magoya bayanta, ta shaida wa wakilan jam'iyyar cewa sun kawar da matsalolin da ke dankwafe mata a siyasar Amurka.

Tana kara da cewa da wannan zaben da suka mata, sun karya lagon siyasar Amurka da suka bude kafar da aka samu kallabi tsakanin rawwuna, sun kawar da shinge da ke hana mata kai labari a siyasar kasar.

A lokacin bude taron jam'iyyar dai magoya bayan Sanata Bernie Sanders sun fice daga wurin, a lokacin da ya ya fito fili ya yi mubaya'a Misis Clinton.

Shi ma mijin 'yar takarar, tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ya yi jawabi a wajen taron inda ya ba da shaida a kan halayen maidakinsa, tun daga zamanin haduwarsu a matsayin saurayi da budurwa zuwa kasancewarsu miji da mata da sauran kyawawan dabi'u da halayen da ya ce tana da su, don hake yake ganin ta dace ta zama shugabar Amurka.

Misis Clinton dai ta samu adadin kuri'un da ake bukata ne lokacin da aka kidaya kuri'ar wakilai jihar South Dakota, inda ta samu kuri'a 2,382.

Sauran batutuwan da suka mamaye rana ta biyu ta babban taron sun hada da maganar wariyar jinsi da bukatar kamanta adalci, kamar yanda wadannan batutuwa suka mamayi babban taron jam'iyyar Republican da aka yi a makon jiya.