Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nigeria: 'Nakasassu ma mutane ne'

A Nigeria, nakasassu sun yi kira ga 'yan majalisar wakilai sun hanzarta kammala aiki a kan kudirin doka da zai saukaka rayuwa a gare su.

Tuni dai majalisar dattawa ta amince da kudurin dokatar da zai haramta duk wani nuna bambanci ko kyama ga nakasassu da kuma samar da abubuwan da za su saukaka musu zirga-zirga da sauran hidimomin rayuwar yau da kullum.

Mohammed Abdu Tudun Wada ya soma da tambayar Musbahu Lawan Didi shugaban kwallon guragu na Nigeria, ko me dokar ta ƙunsa:

Labarai masu alaka