Kun san kasashen da suka fi dogayen mutane?

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani sabon bincike ya nuna cewa maza a kasar Netherlanders da mata a kasar Latvia su suka fi tsawo a duniya.

Binciken ya nuna cewa akasarin 'yan kasar ta Netherlanders suna da tsawon santimita 183, yayin da matan kasar Latvia ke da tsawon santimita 170.

Binciken, wanda aka wallafa a mujallar eLife, ya yi nazari ne kan girman mutane a kasashe 187 tun daga shekarar 1914.

Ya gano cewa mazan kasar Gabashin Timor ne suka fi gajarta a duniya, inda suke da tsawon santimita 160.

Kazalika, mata 'yan kasar Guatemala su suka fi gajarta a duniya, inda binciken ya ce bayanan da aka samu shekara dari da suka wuce sun nuna cewa mace 'yar shekara 18 a kasar ba ta wuce tsawon santimita 140. Yanzu kuma ba sa wuce santimita 150.

Binciken ya kuma gano cewa maza 'yan kasar Iran da mata 'yan kasar Koriya ta kudu sun fi saurin girma, inda girmansu ke karuwa da fiye da santimita 16 zuwa santimita 20.

Kasashen da suka fi dogayen maza a shekarar 2014:

 • Netherlands (12)
 • Belgium (33)
 • Estonia (4)
 • Latvia (13)
 • Denmark (9)
 • Bosnia and Herzegovina (19)
 • Croatia (22)
 • Serbia (30)
 • Iceland (6)
 • Czech Republic (24)

Kasashen da suka fi dogayen mata a shekarar 2014:

 • Latvia (28)
 • Netherlands (38)
 • Estonia (16)
 • Czech Republic (69)
 • Serbia (93)
 • Slovakia (26)
 • Denmark (11)
 • Lithuania (41)
 • Belarus (42)
 • Ukraine (43)

Labarai masu alaka