Tsohon ɗan majalisa ya kai hari a Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al-Shabab na son kifar da gwamnatin Somalia

Kungiyar al-Shabab da ke Somalia ta ce wani tsohon dan majalisar dokokin kasar na cikin 'yan bindiga biyun da suka kai harin kunar-bakin-wake a Mogadishu, babban birnin kasar.

Al-Shabab ta ce Salah Nuh Ismail, mai shekara 53, na cikin 'yan kunar-bakin-waken da suka kashe mutum 13 a kusa da babbar kofar shiga filin jirgin saman kasar.

Salah Nuh Ismai, wanda ake yi wa lakabi da Salah Badbado, ya yi murabus daga mukaminsa na dan majalisa a shekarar 2010 bayan ya bayyana 'yan majalisar da cewa "kafirai" ne.

Al-Shabab dai na yaki ne domin kawar da gwamnatin kasar wacce majalisar dinkin duniya ke mara wa baya.

Babban filin jirgin saman na Mogadishu yana cikin wuraren da ke da matukar tsaro, saboda yanki ne da ofishin kungiyar Tarayyar Afirka da wasu ofisoshin jakadancin manyan kasashen duniya suke.

Labarai masu alaka