Indiya: An lakada wa wasu mata duka kan nama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mabiya addinin Hindu na bauta wa saniya a Indiya

An lakada wa wadansu mata biyu duka wadanda ake zargin suna dauke da naman shanu a wata tashar jirgin kasa a jihar Madhya Pradesh da ke Indiya.

'Yan sanda sun ce zauna-gari-banza ne suka tare matan, wadanda Musulmai ne, bayan da wasu da ke ikirarin su 'yan kato-da-gora ne masu sa ido a kan masu amfani da naman shanu suka kai musu labari.

Amma bayan an yi bincike sai aka gano cewa naman na …ďauna ne, don haka yanzu an sassauta wa matan tuhumar da ake musu ta daukar nama mai yawa ba tare da samun lasisi ba.

Bidiyon dukan matan da turmusa su a kasa da aka yi ya bazu tamkar wutar daji a intanet.

Mabiya addinin Hindu sun dauki saniya abin bauta, hakan ya sa yanka shanu ya zama haramun a mafi yawan jihohin Indiya.

Labarai masu alaka