Karancin fursunoni zai sa a rufe gidajen yari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Raguwar aikata laifuka a Netherlands yasa an samu karancin fursunoni

Kasar Netherlands za ta rufe gidajen yari 19 nan da 'yan shekaru masu zuwa sakamakon karancin fursunoni da kuma yawan kudin da ake kashewa wajen kula da gidajen.

Karancin fursunonin dai ya samo asali ne daga raguwar aikata laifuka da aka samu a kasar, wanda hakan ya jawo gidajen yarin suka zama tamkar kangwaye.

Kafar yada labarai ta kasar ta ce wani dalilin kuma da ya jawo karancin fursunonin shi ne yadda alkalai ke yanke wa masu laifi hukuncin gajeren zama a gidan yari.

Sai dai rufe gidajen yarin zai sa ma'aikatan wajen 1,900 su rasa aikinsu.

Ba wannan ne karon farko da kasar Netherlands ta fara rufe gidajen yari ba; ko a shekarar 2009 ma ta rufe guda takwas ta kuma sake rufe wasu 19 a 2014.

Hakan ce ma tasa wasu kasashen irin Norway suka mayar da fursunoninsu 1,000 Netherlands din don a samu raguwar cunkuso a nasu gidajen yarin.