Ana 'rashin adalci a daukar ma'aikata'

Wasu masu macin rike da kwalayen da ke dauke da sakonninsu
Bayanan hoto,

Wasu masu macin rike da kwalayen da ke dauke da sakonninsu

Wasu 'yan Najeriya sun gudanar da wani maci a babban birnin kasar Abuja, domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira rashin adalci wajen daukar aiki.

Masu macin karkashin inuwar wata kungiya mai suna Citizen of Impact, sun ce ana daukar 'ya'yan manya ne kawai aiki a asirce a manyan hukumomin kasar.

Sun kuma koka cewa hakan tasa ana barin 'ya'yan talakawa na gararamba kan tituna babu aikin-yi.

Masu macin sun gabatar da koke-koken nasu ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayyar kasar.

Sakonni nasu sun hada da cewa, ''Najeriya tamu ce duka ba ta 'ya'yan masu mulki ba kawai,'' da kuma mai cewa, ''rashin adalci wajen daukar aiki keta hakkin bil'adama ne.''

Masu zanga-zangar lumanar sun ce sun gano an yi daukar aiki a asirce a wasu manyan ma'aikatu kamar su babban bankin kasar CBN, da hukumar tara kudaden shiga ta tarayya FIRS, da kuma hukumar kula da gidajen yari ta kasa.

A don haka suka bukaci gwamnati da ta dakatar da shugabannin wadannan hukumomi har sai an yi bincike kan lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Sun kara da cewa suna bukatar a soke wadannan daukar aiki da aka yi a fito da sabon tsari yadda kowa zai iya nema ta hanyar gwada kwazonsa.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsare-tsare, Ibrahim Bafatel, wanda shi ne ya saurari koken nasu ya ce, ya ji dadin gabatar da kokensu da suka yi, ya kuma ba su hakuri cewa irin wannan kan faru ba sanin gwamnati.

A karshe ya ba su tabbacin gabatar da kukansu ga shugaban kasa.