Indonesia za ta harbe 'yan Nigeria hudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An ga motocin daukar marasa lafiya da akwatunan saka gawa na dosar tsibirin da za a aiwatar da kisan

A ranar Alhamis ne kasar Indonesiya ta yi watsi da matsin-lambar da take fuskanta daga kasashen duniya da kuma rokon da ake mata kan hukuncin kisa da ta yankewa wasu masu safarar miyagun kwayoyi 14.

Cikin mutanen da aka yankewa hukuncin har da 'yan Najeriya hudu da kuma 'yan Pakistan da Indiya da Zimbabwe da kuma 'yan Indonesiyar.

Ministan Shari'a na kasar Muhammad Prasetyo ya ce an kebe mutanen su kadai a wani gidan yari da ke kan wani tsibiri, inda a can ne kasar ke zartar da hukuncin kisan da take yi.

Hukumomin kasar ta Indonesiya dai, sun kammala shirin kashe wadannan mutane.

Rahotanni sun ce ana ganin motocin daukar marasa lafiya da akwatunan saka gawa na dosar tsibirin, da kuma jeran gwanon motoci dauke da wadanda hukuncin ya hau kansu, da 'yan sanda da kuma masu bayar da shawara ta bangaren addini.

Shugaba Joko Widodo na kasar ya yi imanin cewa, kasar na fuskantar yawan shan miyagun kwayoyi, kuma lamarin na bunkasa fiye da kima.

Wannan shi ne kisan masu safarar miyagun kwayoyin 'yan kasashen waje masu yawa da shugaba Widodo zai aiwatar tun hawansa kujerar mulki a 2014 .

Kisa na baya-bayan nan da aka aiwatar kan masu safarar muyagun kwayoyi shi ne a watan Afrilun 2015, lokacin da aka kashe wasu mutane takwas da aka yankewa hukuncin kisa.

Mutanen sun hada da 'yan kasar Australiya biyu, abun da ya jawo guna-guni daga kasashen duniya.

Labarai masu alaka