Italiya za ta hana 'yan cirani tafiya mai hadari

Hakkin mallakar hoto MARINA MILITAREREUTERS
Image caption 'Yan cirani na kasada da rayuwarsu wajen tsallake Bahar Rum don zuwa Turai

Gwamnatin Italiya ta kaddamar da wani shiri na amfani da kafofin sadarwa daban-daban domin hana 'yan cirani daga Arewaci da Yammacin Afrika yin tafiyar nan mai hadarin gaske, daga tekun Bahar Rum zuwa Turai.

Gwamatin Italiyar za ta yi amfani da shafukan intanet da gidan talibjin da rediyo da kuma kafofin sada zumunta wajen rarraba labarin 'yan cirani, da suka yi bayani a kan halin da suka shiga a hanun masu safarar mutane da kuma ketara teku mai hadari sosai.

Magajin garin Palermo, Leoluca Orlando, ya sahidawa BBC cewa tsibirin zai cigaba da yin marhabin da mutane da suka shigo cikin garin domin neman mafaka.

Ya ce dubban mutane sun fuskanci azabtarwa saboda sun kokarin ganin cewa ba a kashe su a kasashensu ba.