Al'amura na kara dagulewa a majalisar wakilan Najeriya

Image caption Ana tonon silili a kan kasafin kudin bana

A Nigeria, wa su 'yan Majalisar wakilai suna ci gaba da tonon silili dangane da badakalar kasafin kudin bana.

Lamarin dai ya kai ga zarge-zargen aikata ba daidai ba tsakanin kakakin majalisar Yakubu Dogara da Hon. Abdulmumini Jibrin tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi da majalisar ta cire daga kan mukaminsa.

Yanzu dai wasu 'yan majalisar da suka kira kansu Integrity Group sun nemi a gudanar da bincike akan batun.

Kawuna sun rabu a majalisar tsakanin masu goyon bayan shugaban majalisa Yakubu Dogara, da masu goyon bayan tonon sililin da Abdulmumini Jibrin ya yi, da kuma masu ra'ayin cewa duka bangarorin sun aikata ba dai dai ba.

A yanzu haka dai majalisar ta na hutu, to amma wasu na ganin idan ta dawo batun shi ne abin a za a mai da hankali a kai.

Labarai masu alaka