Obama ya bukaci a zabi Hillary

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Trump ya ce yana da kyawawan halaye

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga masu zabe a kasar da su taimaka domin ci gaba da ayyukan da ya fara ta hanyar zaben Hillary Clinton a watan Nuwamba.

Mr Obama ya yaba wa Mrs Clinton a wajen babban taron jam'iyyar Democratic a Philadelphia, yana mai bayyana ta da cewa "ita ce wacce ta fi dacewa" ta shiga fadar gwamnatin kasar.

Ya kara da cewa yanzu Amurkawa za su yi zabi ne tsakanin "fata na gari", wato Hillary Clinton da kuma "fargaba", wato Donald Trump, yana mai bayyana Trump a matsayin mutumin da yake amfani da karkairayi domin cimma burinsa.

Mr Trump dai ya yi wa Obama raddi, yana mai cewa ba haka halayensa suke ba.