An kulle yarinya saboda ta sumbaci wani mutum

Lauyoyinta sun bukaci a kai mata agaji
Bayanan hoto,

Lauyoyinta sun bukaci a kai mata agaji

Mahaifin wata yarinya a kasar Saudiyya ya kulle ta a gida tsawon shekara hudu saboda ta sumbaci wani mutum.

Yarinyar, mai suna Amina Al-Ja'afari, 'yar shekara 21, tana da shaidar zama a kasashe biyu -- Ingila da Saudiyya.

Lauyanta ya shaida wa wata kotu cewa mahaifin yarinyar, Mohammed Al-Ja'afari, ya kulle ta ne ta hanyar sanya sasari a kofar dakinta bayan an aske gashin kanta."

Mahaifinta dai ya musanta zargin.

Yanzu dai lauyan Amina yana son kotun da ke birnin London ta kai wa yarinyar agaji.

An shaida wa kotun cewa Mohammed Al-Ja'afari ya dauki 'yarsa daga Ingila zuwa Saudiyya shekara hudu da suka wuce bayan ya ga take-takenta.