NFF 'ta yi watsi da Siasia'

Image caption Siasia ya ce suna matukar shan wahala

Kocin 'yan wasan Najeriya 'yan kasa da shekara 23 Samson Siasia ya ce hukumar kwallon kafar kasar, NFF ba ta ba shi albashinsa da na mataimakansa ba tun daga watan Janairun da ya wuce.

Siasia ya ce, "Ba a bamu albashi da alawus-alawus ba tsawon wata biyar. Babu wanda ya karbi ko kobo a cikinmu."

"Ya kamata a ba mu albashinmu kafin a fara gasar Olympics saboda muna shan wuya. Ba mu da kudi. Ba a ba mu tikitin zuwa Brazil ba," in ji Siasia.

Kocin ya ce gwamnati ba ta kai musu dauki ba, yana mai cewa ya san idan aka kammala gasar Olympics ba za a saurare su ba.

Gwamnati dai ba ta yi raddi kan wadannan zarge-zarge ba.

Labarai masu alaka