Birtaniya ta jinkirta gina tashar nukiliya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a kashe kimanin dala biliyan 24 wajen gina tashar makamashin nukiliyar

Gwamnatin Birtaniya ta jinkirta shirin gini tashar makamashin nukiliyarta ta farko, 'yan sa'o'i kadan bayan da kamfanin samar da makamashi na kasar Faransa EDF ya amince ya ci gaba da aikin.

Sabon sakatare mai kula da kasuwanci na Birtaniya, Greg Clark, ya ce yana son sake yin nazari ne a kan aiki kafin ya goyi bayan gina tashar.

Wani mai magana da yawun gwamantin Birtaniya ya musanta cewa ministan yana da wata manufa ta daban game da shirin.

Manyan shugabannin kamfanin EDF sun kada kuri'a inda daga cikin su mutum 10 suka amince da fara aikin da zai lakume dala biliyan 24 yayin da mutum bakwai ba su amince ba, kuma mutum guda daga cikin su ya yi murabus yana mai cewa aikin zai jefa kamfanin cikin wani mawuyacin hali na karancin kudade.

Wakilin BBC ya ce jinkirin zai sanya ayar tambaya a kan ikirarin gwamnati cewa kofofin Birtaniya a bude suke ga 'yan kasuwa bayan kuri'ar ficewa daga kungiyar tarayyar turai da aka gudanar a watan jiya.

Labarai masu alaka