Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Akwai barazanar yunwa a Nigeria

Babban jami'in kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya ya yi kashedin cewa bala'in yunwa na iya aukawa wasu sassan Nigeria da kuma yankin tafkin Chadi.

Majalisar dinkin duniyar ta kuma yi kiran a gaggauta daukar matakai wajen shawo kan matsalolin da 'yan gudun hijira ke fuskanta a yankin.

Kusan mutane miliyan uku ne dai rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a Nigeria, da Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Jibrin Santumari shi ne shugaban kwamitin kula da hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa na majalisar wakilan kasar, Isa Sanusi ya tambaye shi ko me zai ce dangane da matsalar yunwa da ake fama da ita a yankin arewa-maso-gabas:

Labarai masu alaka