Lula da Silva zai fuskanci shari'a

Image caption Ana binciken sa ne a badakalar cin hanci da ta shafi kamfani mai na kasar wato Petrobras

Tsohon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva zai fuskanci shari'a kan tuhumar kokarin kawo cikas a shari'a.

Wasu takardu daga babbar kotun tarayya a Brasilia sun nuna cewa an tuhumi Mr Lula ne tare da wasu mutane shida.

An yi ta bincikensa ne a badakalar cin hanci da ta shafi kamfani mai na kasar wato Petrobras.

A watan Mayu ne dai, ministan shari'a na kasar, Brazil (Rodrigo Janot) ya zargi Mr Lula da taka muhimminyar rawa a badakalar da aka kiyasta cewa kamfanin man ya kashe kimanin dala biliyan biyu.

Tsohon shugaban kasar dai ya musanta zargin da ake masa.