An kashe wasu Indiyawa saboda N75

A kasar Indiya, wani ya sare kan wani dan kasar sannan ya makure matar mutumin har ta mutu a kan bashin rupee 15, kwatankwacin Naira 75 a jihar Uttar Pradesh.

'Yan sanda sun ce mutumin da ake zargi da kisan, wanda yana sayar da kayan masarufi ne, ya aikata laifin ne ranar Alhamis bayan ma'auratan sun gaya masa cewa suna bukatar ya dan kara musu lokaci na biyan bashin biskit din da suka karba.

Tuni dai aka kama mutumin.

'Yan sandan sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Press Trust of India cewa lamarin ya faru ne a lardin Mainpuri lokacin da ma'auratan ke kan hanyarsu ta zuwa aiki.

Sun kara da cewa mai kantin, Ashok Mishra, ya tare mata da mijin ne, kana ya bukace su da su biya shi kudin kwalin biskit uku da suka saya wa 'ya'yansu kwanaki kadan da suka wuce.

Rahotanni sun ambato ma'auratan suna shaida masa cewa za su biya shi kudinsa idan suka dauki albashi, amma hakan ya fusata shi inda ya sheka a guje cikin gidansa ya dauko gatari, ya kuma sare kan mutumin sannan ya makure matar.