Cutar Zika ta bulla a Amurka

Image caption An gano cewa cutar ta bulla ne tun makonnin da suka gabata a Miami.

A karon farko, Jihar Florida ta Amurka ta tabbatar da bullar cutar Zika wadda ake dauka daga sauro.

Gwamnan jihar Rick Scott, ya ce mutane hudu na dauke da kwayar cutar Zika a jihar saboda cizon sauro, kuma wannan ya nuna cewa Jihar ta Florida ta zamo jihar farko da aka samu masu cutar a kasar Amurka.

Ya kara da cewa dukkan wadanda suka kamu da cutar babu wanda ya bukaci ya kwanta a asibiti.

Daga cikin wadanda suka kamu da cutar akwai mace guda daya da maza uku.

Daraktan cibiyar da ke kula da cututtuka masu yaduwa a kasar Tom Frieden, ya ce an gano cewa cutar ta bulla ne tun makonni da suka gabata a Miami.