Dalilin tura gwamnonin Najeriya Jamus

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Gwamnoni sun ce suna sane da mawuyacin halin da talakawan kasar ke ciki.

A Najeriya, gwamnonin jihohin kasar sun yi karin haske dangane da shawarar da suka yi ta tura wata tawagar gwamnoni daga shiyyoyi shida na kasar zuwa Jamus.

A cewar gwamnonin, manufar tura tawagar ita ce kulla kawance tare da koyo dabarun inganta rayuwar talakawa.

Gwamnonin dai na mayar da martani ne dangane da korafe-korafen da wasu masu fafutika a kasar ke yi cewa shawarar tura wata tawagar gwamnoni zuwa Jamus wani yunkuri ne na facaka da kudaden al'umma a daidai lokacin da talakawa ke kokawa akan mawuyacin halin da suke ciki.

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce gwamnonin suna sane da mawuyacin halin da talakawan kasar ke ciki kuma gwamnatin tarayya da na jihohi suna daukar matakai don inganta rayuwar jama'a.

Labarai masu alaka