'Mu Haɗu a Minjibir' ta samu cikas

Image caption Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ne dai ya fara fito da jar hula tun bayan Malam Aminu Kano.

Dan takarar jam'iyyar PDP, a zaɓe mai cike da rudani na maye gurbin dan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Minjibir ta jihar Kano, Auwalu Ubale, ya sanar da ficewa daga takarar.

Zaben na Minjibir dai ya biyo bayan mutuwar dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar.

A watan Afrilun wannan shekarar ne dai aka yi zaben amma hukumar zaben kasar ta INEC ta soke shi bisa zargin magudi da tashe-tashen hankula.

A lokacin zaben dai rahotanni sun ce an rasa rayuka tare da jikkata sakamakon tashe-tashen hankulan.

Dan takarar na jam'iyyar PDP, Auwalu Ubale, wanda na daya daga cikin 'yan takara 15, a hirarsa da BBC ya fadi dalilinsa na janyewa daga takarar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mene ne 'Mu Hadu a Minjibir'

'Mu Hadu a Minjibir' wata sara ce irin ta siyasa da mabiya bangaren gwamnan jihar Kano mai ci, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso suka kirkiro da ke nufin raba rainin siyasa a zaben na Minjibir.

Har al'amarin ma ya kai ga fito da wata samfirin hula Ja wadda ake lankwasa ta zuwa gefen kai.

Ana dai alakanta hular da bangaren tsohon gwamnan na Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso domin banbanta tasu jar hular da ta mutumin da ya gaji Kwankwason wato Ganduje wanda ake yi wa kallon ya sanya kafar wando da tsohon uban gidansa.

Sarar ta Mu Hadu a Minjibir dai ta shahara a kafafen sada zumunta a baya-bayan nan, a inda magoya bayan PDP da na APC suke yi wa junansu albishir da raba raini a zaben na Minjibir.

Kusan ma an fi samun irin wannan tsokanar ga juna tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC wato bangaren Ganduje da na Kwankwaso.

Labarai masu alaka