Tayyip Erdogan ya zargi MDD kan juyin mulki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Magoya bayan Erdogan a Turkiyya

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin kasashen Turai bisa rashin nuna damuwarsu dangane da yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyyar.

A yayin nuna alhini dangane da mutane rikici lokacin yunkurin juyin mulkin ya shafa, mista Erdogan ya ce babu ruwan kasar tasa da duk wadanda suke nuna damuwarsu dangane da makomar mutanen da suke kitsa juyin mulkin.

Kawo yanzu dai wani babban jami'in sojin Amurka, ya kore yiwuwar hannun Amurkar a yunkurin juyin mulkin.

Yawancin kasashen yammacin duniya wadanda suke kawance da Turkiyya sun yi Allah-wadai da yunkurin juyin mulkin amma kuma sun nuna damuwarsu dangane da abin da ya biyo bayan juyin mulkin.

Mista Erdogan dai ya ce zai janye kararrakin da ya shigar a kotu, a inda yake zargin wasu mutane da cin zarafinsa.

Akalla akwai shari'u 2000 da aka yi a tsawon shekaru biyu sakamakon cin zarafin shugaban.

A ranar 15 ga watan Yulin 2016 ne dai wasu sojoji suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Tayyip Erdogan, al'amarin da bai yi nasara ba.

Labarai masu alaka