UNICEF zai ci gaba da kai dauki Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira a Dikwai, Najeriya

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya-UNICEF ya ce zai ci gaba da bayar da agajin jin kai ga miliyoyin yara da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya duk da harin da aka kai kan ayarin shi.

Da farko asusun ya sanarda dakatar da ci gaba da kai daukin na wucin gadi a yankin, saboda kwantan bauna da mayakan Boko Haram suka yi wa ayarin shi ranar Alhamis.

Mutane uku ne suka jikkata a harin, wanda ya auku lokacin da ayarin ke dawowa daga Bama inda rahotanni ke cewa yara na mutuwa saboda rashin abinci da magunguna.

A cikin wata sanarwa, Jami'in UNICEF a Najeriya, Jean Gough ya ce zasu ci gaba da bayar da agajin jin kai kamar yadda suka saba a Maiduguri.

Ya ce "muna ci gaba da yin kira a kara azama wajen taimaka wa mutanen da ke cikin mawuyacin hali a fadin jihar. Ba za mu bar wannan hari ya hana mu kai wa ga fiye da mutane miliyan biyu dake cikin bukatar agajin jin kai ba".

A karin bayanin da ta yi, mai magana da yawun asusun, Doune Porter ta ce a iya cikin birnin Maiduguri ne asusun zai ci gaba da bayar da agaji.

Ta ce asusun ya dakatar da kai daukin ga wasu garuruwa dake wajen birnin.

Labarai masu alaka