'Tafiye-tafiyenmu ba ɓarnar kudi ba ce'

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Gwamnonin sun ce tafiyar za ta amfani talakawa ne

Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi karin haske dangane da tura wata tawagarsu daga shiyyoyi shida na kasar zuwa kasar Jamus.

A cewar gwamnonin, manufar tura tawagar ita ce kulla kawance tare da koyo dabarun inganta rayuwar talakawa.

Gwamnonin dai na mayar da martani ne dangane da korafe-korafen da wasu masu fafutika a kasar ke yi, cewa shawarar tura tawagar gwamnaoni zuwa Jamus wani yunkuri ne na facaka da kudaden al'umma a daidai lokacin da talakawa ke kokawa a kan mawuyacin halin da suke ciki.

Haka kuma gwamnonin sun ce cikin batutuwan da za su duba a Jamus har da na yadda za a inganta wutar lantarki a kasar.

Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce lamarin ba haka yake ba.

Gwamnan Nejan ya shaida wa Yusuf Tijjani cewa tafiyar talakan Najeriya za ta amfana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti