An kai hari ofishin 'yan sanda a Mogadishu

Jami'ai a Somalia sun ce an kai hari a wata shedkwatar 'yan sanda a Mogadishu babban birnin kasar.

Akalla mutane gome sha uku ne suka mutu da suka hada da fararen hula biyar.

Ana tsammanin bakwai daga cikin wadanda suka mutun maharan ne.

An ji karar fashewar abubuwa, tare da ganin hayaki na tashi sama, bayan 'yan kunar bakin wake sun kutsa da motoci biyu dake makare da bama-bamai, sashin binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan.

Rahotanni sun ce wasu 'yan bindiga sun yi yunkurin dannawa cikin ginin bayan fashewar bama-baman.

Kungiyar Al-Shabab ta ce ita ke da alhakin kai harin.

Labarai masu alaka