"Donald Trump ya jahilci addinin Musulunci"

Image caption Dan takarar shugabancin Amurka na Republican, Trump

Mahaifiyar wani sojan Amurka Musulmi da aka kashe a Iraki, ta caccaki dan takarar shugabancin Amurkan karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, bayan ya muzanta ta a wurin babban taron jam'iyyarsa.

A wata hira da ta yi da jaridar Washington Post, Ghazala Khan ta bayyana Mista Trump a matsayin mara ilimi kan addinin Musulunci da sadaukar da kai.

Mista Trump ya nuna cewa an ki a bar Misis Khan ta yi magana a wurin taron, bayan ta tsaya kusa da mijinta, lokacin da mijin nata ya soki Mista Trump a wani jawabi mai sosa rai.

Misis Khan ta ce duk da rashin maganarta a wurin, mutanen da ke kallo sun fahimci irin bakin ciki dake tare da ita.

A cikin makon da ya gabata, mijinta, Khizr Khan ya shaidawa 'yan jam'iyyar Democrat cewa Mista Trump bai taba sadaukar da kansa ga kasarsa ba.

Ya ce dansa, ya sadaukar da rayuwarsa ga Amurka, kuma inda don ta Donald Trump ne, da bai ma iya zuwa Amurkan ba.