An tsige Firai Ministan Tunusia

Habib Essid masanin tattalin arziki ne da ya samu horo a Amurka

Asalin hoton, B

Bayanan hoto,

Habib Essid masanin tattalin arziki ne da ya samu horo a Amurka

'Yan majalisa 118 ne suka kada kuri'ar rashin amincewa da Firai ministan Tunusiya Habib Essid, yayin da uku suka kada masa kuri'a, sannan 27 suka kauracewa zaben.

Firai ministan dai wanda aka jima ana takaddama a kansa ya sha fuskantar kiraye-kirayen ya yi murabus a baya-bayan nan.

Ana dai ganin rashin bunkasar tattalin arziki da rashin samun wani sauyi a fagen siyasa su ne suka sa aka kada masa kuri'ar.

Kuri'ar da aka kada wa gwamnatin dai ta zo ne bayan an shafe watanni ana kai ruwa rana dangane da makomar firai ministan, bayan matsin lambar da shugaban kasar yake masa na cewa ya sauka.

Firai minista Habib Essid ya dai ki sauka duk da matsin lambar, yana mai cewa yana mutunta hanyoyin da doka ta tanada, don haka ya ce a bar 'yan majalisa su yanke hukunci a kan makomar tasa.

Wasu masu sharhi na ganin matakin kada kuri'ar tsige firai ministan sakamako ne na yadda ya juya wa 'yan siyasa baya.

A bayabayan nan Essid ya zargin manyan jam'iyyu da cewa suna kokarin tursasa shi ya sauya wasu ministoci, abin da shi kuma ya yi wa kememe.

Gwamnatin ta Habib Essid ta zo karshe ne bayan shekara daya da rabi da kafa ta.