Mutane 16 sun mutu a hadarin balan-balan a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne hadarin kumbon balan-balan mafi muni a Amurka

Mutane goma sha shida sun mutu a Amurka, yayin da wani Kumbon balan-balan da suke ciki ya kama da wuta a sararin samaniya.

Sashin kiyaye hadura na jihar texas ya ce babu wanda ya tsira daga mutanen wadanda suke wani shawagi na nishadi a cikin kumbon, wanda ya fado ya kuma kone kurmus a sararin Lockhart

Shedu dai sun ce sun ga kumbon ya na katantanwa a sama, ya kuma hadu da wayar wutar lantarki, sannan ya kama da wuta.

Wannan dai shi ne hadarin kumbon balan-balan mafi muni da aka taba samu a tarihin Amurka.

Har yanzu dai hukumomi a jihar ta Texas ba su gano musabbabin hadarin ba, sai dai an kaddamar da bincike