An kama tan bakwai na hodar iblis a Bolivia

Hodar iblis da jami'an tsaro suka kama.
Image caption 'Yan sandan sun ce Amurka ake niyyar safarar hodar iblis din a lokacin da aka cafke ta.

'Yan sanda a Bolivia sun kame fiye da tan bakwai na hodar Iblis da akai ammana da cewa za a ci kasuwar ta ne a Amurka.

An dai boye miyagun kwayoyin a cin wata katuwar motar dakon kaya da a tsaunukan da za su sada ka da gabar tekun China ta kasar.

Wani jami'in gwamnatin Bolivia ya ce an cafke mutane uku da ake zargi da safarar miyagun kwayoyin, an yi kiyasin hodar iblis din za ta kai kusan dala miliyan dari hudu.

Ko a watan junairun da ya wuce, hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasar ta cafke tan hudu na hodar iblis da aka boye a cikin ma'adinan da aka hako.

Labarai masu alaka