Za a rufe kurkuku a Costa Rica

Fursunoni
Image caption Alkalin ya dauki matakin rufe gidan ne saboda fursunoni sun yi yawa a cikin sa.

Wani alkali ya bada umarnin a rufe daya daga cikin gidajen kason kasar Costa Rica mai cinkoson jama'a.

Mai shari'a Roy Murillo yace gidan kason San Sebastinian da ke babban birnin kasar San Joe an gina shi ne dan a tsare fursunoni dari shida kacal, amma a halin yanzu adadin wadanda ke gidan ya rubanya hakan.

Ya kara da cewa fursunonin na cikin mawuyacin hali, kuma hakan barazana ce ga kasar kan ajiye fursunonin.

Yawancin dai wadanda ake tsare da su ba a yanke musu hukunci ba su na jiran tsammani ne.

Ko a farkon wannan shekarar sai da wani alkali ya rage yawan fursunonin da ke wani gidan kaso a Costa Rica, ta hanyar yiwa wasu daga cikin su afuwa.

Amma sai 'yan adawa suka soki lamirin gwamnati da zubawa alkalai idanu suna daukar matakin da suka ga dama, ya yin da 'yan kasar ke fuskantar barazar masu aikata muggan laifuka.