"Donald Trump jahili ne"

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Khizr Khan ya bukaci Mr trump ya karanta kundin tsarin mulkin Amurka da kyau

Mahaifiyar sojin Amurkan nan da aka kashe a wajen yaki a kasar Iraki, Ghazala Khan, ta ce dan takarar shugaban kasar Donald Trump ya jahilci addinin Musulinci shi ya sa ba ya kaunar Musulmi.

Shi dai Mr Trump ya yi wa Ghazala Khan shagube ne a kan shirun da ta yi a lokacin da take tsaye bayan mijinta, wanda ke sukar Mr Trump a wajen babban taron jam'iyyar Democrat a makon jiya.

Mijin nata, Khizr Khan, ya caccaki Mr Trump kan kyamar Musulmi, yana mai cewa idan da ta ire-iren su Mr Trump ne da "Mu Musulmi ba za mu samu damar shiga Amurka ba har ma mu sadaukar da rayuwarmu domin ci gaban ta".

Lamarin dai bai yi wa Mr Trump dadi ba, inda ya yi wa Ghazala Khan shaguben cewa "ta yi shiru ta kasa cewa komai."

Sai dai Ghazala Khan ta ce ba ta yi magana a wancan lokacin ba ne domin tana kallon hoton danta wanda aka sanya a dakin taron, kuma idan har ta yi magana a lokacin za ta iya yin kuka.

A wata hira da ta yi da wani gidan talabijin daga baya, Ghazala Khan ta ce Mr Trump bai san ma'anar Musulinci da kuma sadaukarwa ba.

Ta kara da cewa ita da mijinta sun sadaukar da dansu domin ci gaban Amurka, amma Mr Trump bai sadaukar da kowa ba.

Mr Trump dai ya ce ya sadaukar da abubuwa da dama wajen ci gaban kasar ciki har da samar wa dubban Amurkawa ayyukan yi.

Lamarin dai ya janyo wa dan takarar na jam'iyyar Republican suka daga sassa daban-daban, musamman ganin yadda Amurkawa ke mutunta sojojin da suka yi yaki domin kare mutuncin kasar.

An kashe kyaftin Humayun Khan a wani harin bam a Iraki a shekarar 2014, yana da shekara 27 a duniya.