Amurka ta kai hari kan IS a Libya

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Amurka ta kai hare-hare ta sama sau uku Kenan a Libya

Amurka ta ce ta kai hare-hare ta sama kan ‘yan kungiyar masu da’awar kafa daular Musulunci suke a kasar Libya.

An kai harin ne kan birnin Sirte mai tashar jiragen ruwa, tungar ‘yan kungiyar ta IS.

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ce ta bukaci Amurkar ta kai harin.

Inda a wani jawabin da aka watsa kai tsaye ta gidan talbijin na Libya, Firai minista Fayez Sarraj ya ce an kashe ‘yan kungiyar da dama.

Labarai masu alaka