Ɗan Nigeria ya yi nasara a gasar daukar hoto

Hakkin mallakar hoto oic
Image caption Hoton dan Nigeria da ya lashe gasar ta OIC

Wani dan Nigeria na daga cikin mutanen da suka lashe gasar daukar hoto da ke nuna yadda rayuwa ke kasancewa a lokacin azumin watan Ramadan wacce kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ta shirya.

Sakatariyar kungiyar ta OIC da ke da cibiya a birnin Jeddah ce ta shirya wannan gasa ce da nufin fito da tasirin azumi ta fuskar ibada da taimakon juna.

Mutumin, Sa'idu Abdulkadir Hamdullahi, ya ce ya yi matukar farin ciki da ya zamo cikin zakaru.

Gasar dai ta kunshi masu daukar hoto ne da ba su da kwarewa, kuma an sanya tukwuicin kujerar aikin Hajji ga wadanda suka yi nasara.

Kungiyar ta OIC ta ce wasu kwararrun alkalai ne suka tantance daruruwan hotuna da aka tura musu daga kasashe daban-daban, inda suka zabi shida da suka fi yin fice.

Wannan ne dai karon farko da aka sanya wannan gasa.

Labarai masu alaka