EFCC: Jamila ba ta cika sharadin beli ba

Jamila Tangaza
Image caption Jamila Tangaza tsohuwar shugabar sashen Hausa na BBC ce.

Hukumar yaki da yi ma tattalin arzikin Nigeria zagon kasa EFCC, ta ce tana ci gaba da rike Hajiya Jamilah Tangaza, daraktar sashen kula da mallakar filaye a Abuja, tun daga ranar Laraba.

Kakakin hukumar ta EFCC , ya shaida ma sashen Hausa na BBC cewa ba a bayar da belin Jamilah Tangaza ba.

Ana dai zarginta ne da karkatar da wasu kudade naira miliyan dari da hamsin da takwas, lokacin da take mai bada shawara ta musamman ga Ministan Abuja.

Hajiya Aisha Larai Musa ita ce shugabar sashen wayar da kai da fadakarwa na hukumar kuma ta kuma shaidawa BBC cewa cikin sharuddan belin na ta akwai daraktocin guda biyu da za su tsaya mata, daya daga ciki ya kasance ya mallaki gida a Abuja, sai kuma za ta bai wa hukumar EFCC fasfo din ta na tafiye-tafiye.

Hajiya Larai ta ce da zarar ta cika wadannan sharuddan za su bada belin ta.

Labarai masu alaka