Boko Haram: An kama 'yan banga a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babu tabbacin takamaiman lokacin da aka kama 'yan bangar

Hukumomi a ƙasar Kamaru sun kama wasu 'yan banga bisa zarginsu da hada baki da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

Kuma an fara bincike domin tantance ko akwai wata alaka a tsakanin 'yan bangar da kuma 'yan Boko Haram ko kuma babu.

Sojoji ne suka kama shugaban 'yan bangan Abdouramane Ali da mataimakinsa, Abba Malloum da wasu 'yan ƙato da gorar da dama.

An kama mutanen ne a garin Djakana da ke yankin arewa mai nisa, kuma an mika su ga hukumomi a garin Kolofata.

'Yan ƙato da gorar dai suna taimaka wa ne wajen yaki da 'yan ƙungiyar Boko Haram wadanda ke kai hare-hare a yankin na kamaru da ke maƙotaka da Najeriya.