Wani ɗan Nigeria na haɗa aure tsakanin masu HIV

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wani dan Najeriya, Emmanuel Michael Ugochukwu ya fito da wani tsari inda yake nemo wadanda suke dauke da HIV ya hada su aure.

Mista Ugochukwu ya shaida wa BBC cewa ya dauki wannan mataki ne saboda kawo karshen ƙyamar da ake nuna wa masu dauke da cutar ta HIV.

Ya kara da cewa yana rubuta lambar wayarsa a muhimman wurare ta yadda masu sha'awar yin auren za su kira shi domin samun bayani, kuma daga nan zai hada su.

A cewarsa, ya hada masu dauke da HIV kimanin 2000 aure.

A yawancin lokuta dai kyamar ta fi tsanani musamman dangane da batun aure da haihuwa.

Labarai masu alaka