'Yan tasin Uber sun yi bore a Kenya

Hakkin mallakar hoto

'Yan tasi da ke aiki da kamfanin hayar motoci na intanet, wato Uber, sun yi zanga-zangar neman ƙarin albashi a ƙasar Kenya.

Matuka motocin hayar da yawansu ya kai 150 sun yi zaman dirshen ne a kofar kamfanin da ke Nairobi dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce kan korafe-korafensu.

Masu boren dai sun nuna rashin amincewarsu ne kan rage kudaden kamfanin ke cajin mutane.

A makon jiya ne dai Uber ya sanar da rage farashin da yake caji domin kiran kasuwa.

Mutane na hayar motocin kamfanin ne ta hanyar latsa wata manhaja a wayar salularsu, kuma ana zargin kamfanin da cewa ya rage kasuwar sauran motocin haya a biranen duniya.

Labarai masu alaka