An ci gaba da biyan tsoffin mayakan Niger Delta alawus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hare-haren 'yan ƙungiyar Niger Delta Avengers sun gurgunta harkar haƙo mai a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ta ci gaba da biyan tsofaffin masu tayar da ƙayar baya na yankin Niger Delta alawus-alawus dinsu bayan tsaikon da aka samu na watanni hudu.

Shugaban hukumar da ke kula da shirin afuwa ga 'yan bindigar yankin da suka ajiye makamai, Birgediya Janar Paul Boroh ya ce an samu tsaikon ne sakamakon matsin tattalain arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Sai dai a ranar Talata gwamnatin ta ci gaba da biyan kudaden alawus din na naira 65,000 a duk wata ga duk wanda ke amfana da shirin.

Baya ga alawus, shirin ya kuma tanadi horar wa ga tsoffin 'yan bindigar, a yunkurin kawo karshen hare-hare kan bututan mai a yankin.

Mista Boro ya kuma bayyana wa BBC cewa gwamnatin ƙasar na da niyyar kawo karshen shrin afuwar nan da shekaru biyu masu zuwa.

Haka kuma za ta fito da wani shiri "na a koma gona" ga masu tayar da kayar bayan da a yanzu suke kai hare-hare kan kamfanoni da bututan mai da na iskar gas a yankin.

Kashi 70 cikin dari na kudin shigar Najeriya ya dogara ne kan danyan man da take fitarwa kasashen waje.

Labarai masu alaka