Obama ya jefa Amurka cikin bala'i — Trump

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama ya ce Amurkawa za su yi da-na-dani idan suka zabi Trump

Donald Trump ya ce shugabancin Barack Obama bai kawo wa Amurka komai ba sai "bala'i".

Mista Trump ya yi wannan raddi ne bayan Shugaba Obama ya ce Trump din ba mutum ne da zai iya shugabanci ba.

Trump ya shaida wa gidan talabijin na Fox News cewa Obama "shugaba ne mai rauni, wanda bai iya mulki ba.

Mista Obama dai ya yi shagube ga jam'iyyar Republican, yana mai cewa bai ga dalilin da zai sa 'yan jam'iyyar su rika yi wa Trump yakin neman zabe ba a daidai lokacin da suke caccakarsa saboda rashin dacewarsa ya shugabanci kasar.

Mista Trump dai ya ce ba zai bayar da goyon baya a sake zaben kakakin majalisa Poul Ryan ko Sanata John McCain ba a zaben fitar da gwani ba.

A bangare guda kuma Richard Hanna na jam'iyyar Republican shi ne na farko a majalisa da yace zai marawa abokiyar hamayyar Mista Trump ta jam'iyyar Democrats Hillary Clinton baya.