Boko Haram 'ta yi sabon shugaba'

Image caption Ƙungiyar Boko Haram ta kuma ci gaba da farfaganda a shafukan sada zumunta

Wata mujalla ta ƙungiyar masu da'awar kafa daular Musulunci ta IS ta sanar da Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon shugaban reshenta da ke yammacin Afrika, wato Boko Haram.

Hakan dai na nufin ya maye gurbin Abubakar Shekau, wanda tun da ya bayyana a wani faifan bidiyo a watan Agustan bara ba a kara jin duriyarsa ba.

A baya dai Abu Musab shi ne kakakin ƙungiyar ta Boko Haram, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyon da ƙungiyar ta fitar a watan Janairun 2015.

Sai dai farmakin da rundunar sojin Najeriya ke kai wa a kan Boko Haram ya gurgunta ayyukan ƙungiyar, ko da yake a baya-bayan nan ƙungiyar ta ƙara ƙaimi wajen hare-haren da take kaiwa.

Mayakan na Boko Haram sun kashe fiye da sojoji 20 a yanki Diffa na Jamhuriyyar Nijar, Inda a makon jiya ma sun kai hari ta hanyar kwanton ɓauna a kan ayarin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya.

Labarai masu alaka