An kai hari birnin London

'Yan sanda a wurin da aka kai harin
Image caption Jami'an tsaro na kyautata zaton matashin ya na da matsala tabin hankali.

Wata mace ta rasa ran ta, ya yin da wasu mutane biyar suka jikkata a harin da wani matashi ya kai da wuka a tsakiyar birnin London.

'Yan sanda sun yi amfani da na'urar da ake azabtar da mutum da wutar lantarki wajen cafke matashin mai shekaru 19, da ya kai harin a dandalin Russell.

'Yan sandan sun kara da cewa binciken farko da aka yi kan harin ya nuna cewa matashin ya na da tabin hankali, amma duk da haka dole ne a binciki batun ta'addanci a dalilan da suka sanya aka kai harin.

Kakakin 'yan sanda a birnin ya ce a yau Alhamis za a kara yawan jami'an tsaro a titunan birnin London.