Matar shugaban Nicaragua za ta zama mataimakiyarsa

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Daniel Ortega ba ya fitowa bainar jama'a sosai

Shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega ya zabi matarsa domin zama mataimakiyarsa a zaben shugaban kasar da ya tsaya a karo na uku.

Dama dai matar tasa, Rosario Murillo, tana da babban mukami a kasar domin kuwa ita ce mai magana da yawun shugabanb kasar, kuma ana yi mata kallo a matsayin wadda ke taya shugaban gudanar da mulki.

Kusan kullum sai ta bayyana a gidan talabijin na kasar domin bayar da bayani kan wasu shirye-shiryenta.

Shi kuwa Shugaba Ortega ba kasafai yake fitowa bainar jama'a ba.

Wasu dai na sukar matar da mijinta kan wannan batu, suna masu cewa sun mayar da mulkin kasar kamar gadon gidansu.

Rosario Murillo, wacce ta haiha wa shugaban kasar 'ya'ya bakwai, ta kware wajen magana da harshen Turanci da Faransanci, baya ga matsayinta na fitacciyar marubuciyar wakoki.

Ta kuma yi fice wajen sanya tufafin kawa da gwala-gwalai wadanda aka saba gani a shekarun 1960.

A watan Nuwamba ne dai aka gudanar da zabe a kasar.