ANC na fuskantar barazana a Afirka ta kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zuma ya sha musanta zargin cin hanci

Jam'iyyar ANC ta Afirka ta kudu na fuskantar shan kayen da bata taba yi ba a zabe tun bayan mulkin masu nuna wariyar launin fata.

Ya zuwa yanzu, sakamakon zaben kananan hukumomin da aka yi ya nuna cewa ta samu kashi 50 cikin dari, wata kasa da kashi goma a kan nasarar da ta yi a zaben kananan hukumomin da aka yi shekara biyar da suka wuce.

Babbar jam'iyyar hamayya, the Democratic Alliance, ta samu kusan kashi 30 cikin 100, inda ta yi nasara a manyan birane irin su Johannesburg da Port Elizabeth.

Tana kasa tana dabo kan ikirarin da ANC ta yi na lashe zaben yankin Nkandla, inda Shugaba Jacob Zuma ya fito.

Rashin ayyukan yi da kuma zarge-zargen cin hanci da ake yi wa Jacob Zuma sun ragewa jam'iyyar ta ANC farin jini.

Labarai masu alaka