APC ta ja kunnen Abdulmumini Jibrin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi tsohon shuagaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilan kasar, da ya daina maganganu a kafafen yada labarai kan rikin majalisar.

Jam'iyyar ta nemi Abdulmumini Jibrin, wanda ke wakiltar Bebeji da Kiru a jihar Kano, da kada ya kara cewa komai game da rikicin a kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta.

Shi dai dan majalisar ya wallafa wasu bayanai, sannan ya rinka hira da kafafen yada labarai, inda yake zargin shugabannin majalisar da almundahana a kasafin kudin kasar.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga mukamin shugaban kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.

A wata wasika da shugaban APC mai kula da shiyyar Arewa, Senata Lawal Shu'aibu ya aikewa dan majalisar, ya yabawa Mista Jibrin game da amsa gayyatar jam'iyyar da ya yi ranar Talata.

Sai dai ya ce jam'iyyar ta APC ba ta ji dadin abin da ke faruwa a majalisar ba kan badakalar kasafin kudin.

Kafin jam'iyyar ta gana da Mista Jibrin, sai da ta tattauna da Kakakin Majalisar Yakubu Dogara, a wani yunkuri na shawo kan lamarin.

A baya dai, dan majalisar yana daya daga cikin na hannun damar shugaban majalisar.

Labarai masu alaka