Ejike Mbaka ya caccaki Buhari

Hakkin mallakar hoto Nigeria Government
Image caption Mbaka ya ce 'yan Najeriya na cikin kuncin rayuwa

Fitacccen mai wa'azin busharar nan na cocin darikar Katolika da ke birnin Enugu a kudu maso gabashin kasar, Rabaran Fada Ejike Mbaka ya soki shugaban kasar Muhammadu Buhari a kan salon shugabancinsa.

Rabaran Fada Mbaka, wanda ya yi wannan suka a wajen wani taro da yake yi shekara-shekara, ya ce 'yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali, kuma idan Shugaba Buhari bai dauki mataki a kan haka ba, zai gamu da fushinsu.

Ya kara da cewa komai ya yi tsada a kasar, yana mai cewa "Masu saye da sayar da kayayyaki na kokawa. Ana korar dalibai daga makaranta yayin da masana'antu ke rufewa. Kazalika 'yan Niger Delta Avengers na kai hare-hare. Idan suka ci gaba da haka za a kasa biyan albashi, za a fada cikin matsanancin hali".

Rabaran Fada Mbaka ya ce mutane da dama na mutuwa saboda mawuyacin halin da suke ciki, yana mai cewa idan al'amura suka ci gaba da wakana kamar yadda suke a yanzu, babu wanda zai sake zaben Shuga Buhari a shekarar 2019.

Limamin cocin, wanda ya rika caccakar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan saboda salon shugabancinsa gabanin zaben shekarar 2015, ya yi kira ga Shugaba Buhari ya sauya yadda yake shugabanci ta yadda 'yan kasar za su samu walwala.

A wancan lokacin dai, Ejike Mbaka ya goyi bayan Muhammadu Buhari domin zama shugaban kasar.

Labarai masu alaka