Ambaliyar ruwa ta ci mutum 76 a Sudan

Hukumomi a Sudan sun ce ambaliyar ruwa da ruwan sama kama da bakin kwarya sun haddasa mutuwar mutane 76 a 'yan kwanakin da suka wuce, yayin da dubban gidaje suka rushe.

A wasu wuraren ma kauyuka sukutum ruwan ya share.

Ambaliyar dai ta shafi 13 daga cikin lardunan Sudan 18.

Ma'aikatar ruwa da noman rani ta ce Kogin Nilu ya yi cikar da bai taba yi ba a fiye da karni guda.

Ana kuma sa ran samun ruwan sama mai yawa.