Ba zan taba yin murabus ba - Dogara

Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan Najeriya
Image caption Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilan Najeriya

Kakakin Majalisar Wakilai ta Nigeria Yakubu Dogara, ya ce ba zai yi murabus ba duk da zargin cusa ayyukan boge a kasafin kuɗin bana da ake yi masa tare da wasu mukarrabansa.

Mista Dogara ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da yayi da Shugaba Muhammadu Buhari a yammacin ranar Juma'a.

Ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa: "Babu inda za ni, domin babu abin da na aikata wanda ya sabawa doka. Ni ban san wani da ya yi kama da cusa ayyukan boge ba".

Babu cikakken bayani a hukumance a kan ganawar da shugabannin suka yi su kadai.

Sai dai ba za ta rasa nasaba da rikicin da ya dabaibaye Majalisar Wakilan ba game da badakalar kasafin kudin ba.

Wani na hannun daman kakakin majalisar ya tabbatar wa BBC ganawar, amma ya ce bai san abin da suka tattauna ba.

Tuni jam'iyyar APC mai mulki ta gana da Mista Dogara da kuma tsohon shugaban kwamitin kasafin kuɗi Abdulmumin Jibrin domin shawo kan rikicin.

Mista Jibrin ya wallafa wasu bayanai, sannan ya riƙa hira da kafafen yaɗa labarai, inda yake zargin shugabannin majalisar da almundahana a kasafin kuɗin.

Sai dai mai magana da yawun Majalisar Wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga shugabancin kwamitin kasafin kuɗi ne ya sa yake furta su.

Labarai masu alaka

Karin bayani