Gobara ta kashe mutane 13 a Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Akalla mutane goma sha uku sun rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a wani wajen shan barasa da ke birnin Rouen a arewacin Faransa.

Wasu mutum shida kuma sun jikkata a gobarar, wadda ta tashi a lokacin da ake bikin murnar zagayowar ranar haihuwa wato birthday party.

'Yan sanda sunce wutar ta tashi ne da tsakar dare, kuma akwai yiwuwar kyanduran da aka kunna akasa a kan cake din partyn ne suka haddasa gobarar.

Mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su na tsakanin shekaru goma sha da ashirin da 'yan dori ne.

Labarai masu alaka